A cikin rahoton wakilin Ofishin Yada Labaran Hauza, Hujjatul Islam Maliki, Mataimakin Shugaban Makarantun Ilmin Addinin Musulunci na Qom, a wani taro kan koyar da ɗa'a a Alƙur'ani da aka gudanar a makarantar Ma'asumiyya, yana naƙalto saƙo daga Ayatullah A'arafi, Shugaban Makarantun Ilmin Addinin Musulunci, ya ce: Ayatullah A'arafi ya jaddada cewa waɗannan tarukan koyar da ɗa'a su ci gaba, kuma mu ma a cikin ɗan gajeren lokaci za mu gabatar da wasu bayanai ga ɗalibai masu daraja.
Malamin na Hauzar Qom ya bayyana asalin maudu'in taron a matsayin "Wajabcin kamanceceniyar ɗalibai da malaman addini da Manzon Allah (SAWA)," inda ya ce: Dole ne malaman addini su zama mutanen da suka fi kama da Manzon Allah (S.A.W); babu wata hanya ta daban.
Mataimakin shugaban Hauzar na Qom, yayin dogaro ga littafin Nahjul Balagha, ya kara da cewa: Daga halayen Manzon Allah (SAWA) akwai cewa yana tunani kafin ya yi
magana; yakan dakata, yayi tunani, sannan ya yi magana. Manzon Allah (S.A.W) bai taɓa yin magana ba tare da tunani ko lura da buƙatun masu sauraro ba.
Yanke Shawara a cikin Sirar Annabi
Hujjatul Islam Maliki, yayin nuni ga halayen Manzon Allah (S.A.W) a cikin zamantakewa, ya ce: "Manzon Allah (S.A.W) ba ya gaggawar yin ayyuka. Da farko yana nazarin sakamako da kuma buƙatun aikin, kuma idan ya yanke shawara, yana aiwatarwa ba tare da jinkiri ba. Wannan hanya, abin koyi ne mai mahimmanci ga rayuwar ɗalibai a daidaiku da kuma cikin jama'a."
Malamin na Hauzar Qom, yayin nuni ga wasu halaye da a ɗabi'a na Manzon Allah (SAWA), ya bayyana cewa: "Manzon Allah (SAWA) koda yaushe cikin murmushi, sai dai a gaban mai zunubi. Yana riga kowa yin sallama kuma idan yana musabaha da wani, baya fara saki hannunsa. Har daukar asuwaki da mataji na daga cikin al'adunsa na yau da kullun, kuma waɗannan halaye masu sauƙi suna iya shiryar da mutane."
Muhimmiyar Ruwaya Game da Magana Mai Hikima
Mataimakin shugaban Hauzar Qom, ya yi nuni ga riwaya daga Ibn Mas'ud wanda aka ruwaito a cikin "Bihar al-Anwar, juzu'i na 74, shafi na 106," ya ce: "Manzon Allah (SAWA) ya ce wa Ibn Mas'ud da abokansa waɗanda suke korafin wahalar rayuwa: 'Ba wanda zai shiga Aljanna face masu haƙuri, kuma ana ba da Aljanna da aiki ne ba da buri ba.'"
Hujjatul Islam Maliki ya fayyace muhimmin sashe na riwayar kamar haka: "Manzon Allah (S.A.W) ya ce wa Ibn Mas'ud: 'Kada ka faɗi wani abu, har sai ka tabbata da shi, ko da ka ji ko ka gani.' Wannan gargaɗin, yanzu a zamanin jita-jita na shafukan sada zumunta, yana da mahimmanci sosai."
Ya kuma bayyana cewa Manzon Allah (S.A.W) ya karanta wasu ayoyin Alƙur'ani don koyar da wannan darasi:
Suratul Isra'i, aya ta 36: "Kada ka bi wani abu da ba ka da masaniya game da shi. Lalle ne, bisa ga wannan, kunne da ido da zuciya, dukkansu za a tambaye su (a ranar Alƙiyama)."
Suratuz-Zukhruf, aya ta 19: "Za a rubuta maganganu na karya, Kuma za a bijiro wa mutane su ranar kiyama".
Suratu Qaf, ayoyi na 16 zuwa 18: "Ubangiji ya na kusa da mutane fiye da yadda suke da jijiyoyin wuya, kuma Mala'iku suna rubuta tare da kiyaye dukkan abin da suka furta".
Mataimakin shugaban makarantun ilmin addinin Musulunci na Qom ya kara da cewa: "Manzon Allah (SAWA) yana so ya koya wa Ibn Mas'ud cewa ya faɗi magana da ilimi, ba bisa zato, ko shakka, ko jita-jita ba. Wannan ita ce hanyarsa ta koya tarbiyya."
Malamin Hauzar ta Qom a ƙarshe, yayin da yake mai jaddada yin aiki da ilimi, ya ce: "Muna fatan Allah Ya ba mu nasara mu kasance masu tsayin daka, a kan hanyar neman ilimi, da kuma yin aiki da abin da muka sani."
Your Comment